Kungiyar Mu Na Wayar Da Kan Al’umma Muhimmancin Mallakar Katin Zabe – Hon Rukayya

Kungiyar Mu Na Wayar Da Kan Al’umma Muhimmancin Mallakar Katin Zabe – Hon Rukayya

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

A lokacin da babban zaben shekarar nan ta 2023 ke ta kara karatowa, Koodinatan Shiyar arewa maso gabas na kungiyar wayar da kan Al’umma Muhimmancin Katin Zabe (Nigeria Voter Union North East) Honurabul Rukayya Robert D. Sallah Cham Jakadiyar Mona, tace kungiyar su na shiga lungu da sako dan Ilmantar da jama’a muhimmancin mallakar katin zabe.

Rukayya Robert, tace dan ganin al’umma sun fito a ranar zabe sun zabi shugabanin da suka dace suna shiga kafafen yada labarai suna ilmantar da Jama’a cewa kowa ya mallaki katin zaben sa domin sai da katin zabe za’a iya zabar shugabanin nagari,

“Da kuri’a Daya za ka iya canja Najeriya wajen zabo shugaba mai nagarta” inji Rukayya

Tace suna hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC wajen shirya tarurruka na masu ruwa da tsaki kan muhimmancin fitowa a karbi katin zabe kamar yadda INEC din ke kira kullum a fito a karbi katin wanda yanzu ake kai wa har rumfunan zabe.

A cewar ta idan suka shiga yankunan karkara suna fadakar da su cewa su dai na yarda ana musu karyar za’a taimake su ana karbar katin zaben su ana basu Taliya ko gishiri ko a basu naira dubu daya, hakan shi ne sun sayar da ‘Yancin su kenan.

Jakadiyar Mona, ta kara da cewa suna fuskantar matsala da Matasa wadanda sune jigon rayuwa wadanda da su ake amfani wajen tada hargitsi a lokacin zabe ana basu kwaya ko yan kudade ana amfani da su suna lalata goben su saboda sune manyan gobe.

Daga nan tace a yan kwanaki da basu wuce Talatin a gudanar da zabe ba idan suka jajirce za’a gudanar da sashin zabe kuma ba tare da hayaniya da bangar siyasa ba.


Tags assigned to this article:
INECon RukayyaRabilu Abubakar

Translate »