Kafin Karfe 2 Na Rana Na Kada DanKwambo Da Sanata Dan Alkali A Zabe – Dan Takarar ADC

Kafin Karfe 2 Na Rana Na Kada DanKwambo Da Sanata Dan Alkali A Zabe – Dan Takarar ADC

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Dan Takarar Kujerar Sanata a Mazabar Gombe ta Arewa mai kananan hukumomi biyar da suka hada da Gombe da Dukku da Kwami da Funakaye da Nafada, Alhaji Ahmed Adamu, na Jam’iyyar ADC yace kafin karfe biyu na rana kyeyar su ta taba kasa saboda duk yafi su cancanta.

Ahmed Adamu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a Gombe inda yace ya fito Takara ne don kawo canji domin su wadannan masu manyan shekarun su zakuda su bai wa Matasa waje domin an gwada su sun gaza dan haka su bada waje Matasa suyi na su.

Yace tsohon gwamnan Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi gwamna an gani me ya manta yake don ya yi Sanata, shi ma Sa’idu Ahmed Alkali sau biyu yana Sanata amma har yanzu yankin sa bai shaida ribar siyasa ba to me suke so su gayawa mutane, su tattara komatsan su Gombe ta arewa sai Ahmed Adamu.

Ya kara da cewa a wannan zabe na 2023 jam’iyyar su ta ADC (African Democratic Congress) za ta bai wa jama’a da yawa mamaki a fadin kasar nan musamman a yankin Gombe ta arewa a jihar Gombe da suke da tabbacin kawo kujerar Sanata.

Alhaji Ahmed Adamu, yace yana da kyawawan manufofi da idan yaci zabe al’ummar yankin sa za su shaida domin a duk fadin jihar Gombe wannan yanki mai kananan hukumomi biyar su aka bari a baya saboda rashin samun wakilci.

“A wasu yankunan karkara a karamar hukumar Dukku da suka hada da Wawa da Zange basu da ruwan sha mai tsafta ba wutar lantarki balle hanya mai kyau da za ta hada su da helkwatar karamar hukumar su, haka ma karamar hukumar Nafada basu da hanya babu abubuwan more rayuwa amma idan aka bashi dama aka gwada shi duk zai share musu hawaye” inji shi.

Ya kuma ce hatta tsadar kayayyakin masarufi da ya Ta’azzara a fadin kasar nan zai hada kai da yan majalisu suyi Doka na dai dai ta farashi dan samawa Talakawa saukin rayuwa.

Daga nan sai ya ja hankalin Yan Najeriya da cewa kar su damu da girma ko kankantar jam’iyya su duba cancanta domin ita jam’iyyar ADC salon ta ma shi ne Musabaha shaidar kaunar jama’a kenan.


Tags assigned to this article:
Sa'idu Ahmed Alkali

Translate »